close

Labarin Wata Bazawara da mijinta

Watarana awani kauye wata bazawara tana da bazawarinta wanda suke shashanci, rannan sai wani daga wani kauyen yazo yace yanasan wannan bazawara. To bayan anyi aure sai yadauke ta yatafi da'ita garinsu. To sai rannan suka hada baki da wancan abokin shashancin nata yace zai yi shigar mata yakawo mata ziyara. ......da yazo sai tace wa mijinta ai kanwar mahaifiyar ta ce tazo sai yayi murna yazo ya gaida ita yaganta kuwa tasha kunshi, sai matar tasa tadau tulu ta tafi rafi debo ruwa.... ...... fitarta kedawuya sai mijinta yazo wucewa... Kwatsam..... sai ya ga wannan bakuwa tayi wawan zama sai kau ya ga ashe namijine!.... haba ai sai gogan naka yadau takobi yabi matar nan tasa rafi a guje.... .....ai ko da matar ta hango shi da takobi a hannu sai kawai ta rafka ihu tana sallallami.....-. Sai gogan naka ya dakata yace me kike wa kuka? Sai tace yanzunna aka aiko min wai duk mazan garin mu sun zama mata, matan kuma sun zama maza. .ai ko da gogan naka ya ji haka sai jikinsa yayi sanyi. Sai yace to wacce kika bari a gida ma ta zama.... Sai kije kigani......

Recent Posts

Navigation

Category